1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun rasa rayukkansu a kauyukkan Sokoto

Abdoulaye Mamane Amadou
February 26, 2019

Akalla mutane 16 ne suka rasa rayukkansu a kauyukkan Rabah da ke Jihar Sokoto a arewacin Najeriya sakamakon wani harin 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/3E8qt
Wahlen und Smartphone in Nigeria
Hoto: DW/K. Gänsler

A Tarayyar Najeriya akalla mutane 16 ne suka rasa rayukkansu a kauyukkan Dalijan, da Kalhu a karamar hukumar Rabah da ke Jihar Sokoto a arewacin kasar

Wannan lamarin dai ya faru ne sakamakon afkawa mazauna kauyen da wasu dauke da makamai da ake kyuatata zaton barayin shanu ne suka yi a daren Litinin, kamar yadda Anas Ghandi wani mazaunin kauyen ya shaidawa wakilinmu na Jihar Sokoto.

Yankin dai na makwabataka ne da Jihar Zamfara da yanzu hakan ke fama da hare-haren 'yan bindinga, wanda akai-akai suke yi wa kauyen na Rabah kutse. Ko a makwannin baya ma dai wasu mutane akalla 10 sun halaka a wani harbi na kan mai uwa da wabi da 'yan bindigan suka yi ta yi a kauyukan .