′Yan bindiga sun hallaka mutane 11 a Najeriya | Labarai | DW | 17.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun hallaka mutane 11 a Najeriya

Ana ci gaba da samun hare-hare masu nasaba da kungiyar Boko Haram cikin yankunan da ke karkashin dokar ta baci na arewacin Najeriya.

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram sun hallaka mutane 11, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.

Lamarin ya faru cikin daren ranar Alhamis a garin Damboa na Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar, yankin da ke zama tungar kungiyar Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai. Tun cikin watan Mayu jihar ke karkashin dokar ta baci, wanda Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa.

Hare-hare masu nasaba da kungiyar sun yi sanadiyar salwantar rayuka masu yawa, tun lokacin da kungiyar ta kaddamar da farmakin a shekara ta 2009.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh