′Yan bindiga na ci gaba da tayar da hankali a Najeriya | Labarai | DW | 20.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga na ci gaba da tayar da hankali a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani gari a jihar Bauchi, sannan rikicin kabilanci ya ritsa da rayuka a jihar Taraba.

Wasu 'yan bindiga sun kaddamar da hare-haren cikin daren wannan Asabar a garin Yana helkwatar karamar hukumar Shira da ke jihar Bauchi cikin yankin arewacin Tarayyar Najeriya, inda suka lalata bankin da ke garin tare da wawushe kudi, sannan sun kona dukiyar mutane masu yawa. An kai harin cikin garin tun da misalin karfe 12.30 na dare har zuwa misalin karfe uku da minti arba'in inda suka ci karensu ba babbaka.

A daya hannun rahotanni daga yankin Wukarinjihar Taraba a Najeriya na bayyana barkewar wani tashin hankali a wani wuri da ake kira Gindin Dorawa mai nisan kilomita 40 da garin Wukarin, rikicin da ake dangantawa da kabilanci da kuma addini.

Cikin daren Asabar ne dai bayanai suka tabbatar da tashin lamarin zuwa wayewar gari wanda ya kai ga kashe-kashe da asarar dukiyoyin da har yanzu ba a tantance ba.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal