1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan awaren Kamaru sun yi garkuwa da mata

May 24, 2023

Gomman mata ne aka yi garkuwa da su a Kamaru, zargin da ya hau kan 'yan awaren nan na yankin rainon Ingilishi na da ke gwagwarmayar neman ballewa.

https://p.dw.com/p/4RjiF
Hoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP/Getty Images

Hukumomi a yankin rainon Ingilishin na Kamaru dai sun ce 'yan awaren da ke dauke da muggan makamai, sun yi matukar azaftar da matan akalla su 30 da suka yi awon gaba da su.

Lamarin wanda ya faru a karshen makon da ya gabata, ya rutsa ne da matan garin Kendjom Keku wanda ke a arewa maso yammacin kasar wanda ke iyaka da Najeriya.

Yanki ne dai da ya yi kaurin suna a bangaren matsaloli masu nasaba da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Yankin rainon na Ingila a Kamaru dai, na dauke ne da mutane da ake gani tsiraru ne, a kasar da galibi ke amfani da harshen Faransanci.