1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Zimbabuwe sun nuna fushi kan zabe

July 11, 2018

'Yan adawa a Zimbabuwe sun afka wa hukumar zaben kasar inda suka sake bayyana bukatarsu ta samar da wasu sauye-sauyen da za su bai wa 'yan kasar zabe na kwarai.

https://p.dw.com/p/31HTR
Simbabwe
Hoto: DW/C. Mavhunga

'Yan adawa a kasar Zimbabuwe sun yi maci zuwa shelkwatar hukumar zaben kasar karo na biyu, inda suka sake bayyana bukatarsu ta samar da sauye-sauyen da za su bai wa 'yan kasar sahihin zabe.

A ranar 30 ga wannan watan na Yuli ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, zabe na farko bayan murabus na tilas da tsohon shugaba Robert Mugabe ya yi a bara.

Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar na jam'iyyar ZANU-PF na fuskantar tsananin adawa daga jam'iyyar MDC.

Dubban 'yan adawar da suka yi macin a wannan Larabar, na dauke ne da wasu allunan da ke tabbatar da matsayinsu na lallai ne a samar da sauye-sauyen da suke so a tsarin zaben na Zimbabuwe.