'Yan adawar Masar sun ce an yi magudi a kuri'ar raba gardama
December 15, 2012Talla
'Yan adawar dai sun ce jam'iyyar 'yan uwa Musulmi ta shugaba Muhammad Mursi ta tafka magudi, baya ga yin amfani da kuri'un da ke bude da kuma yin amfani da wani alkali wajen hana wasu mabiya addinin kirista kada kuri'unsu a wata mazaba da ke birnin Alkahira.
Gabannin wannan kuri'a ta raba gardama dai, an yi ta zanga-zanga da kuma tada jijiyar wuya tsakanin mabiya jami'iyyar 'yan uwa Musulmi wadda ke mulkin kasar da kuma 'yan adawa wanda ba sa goyon bayan gudanar da jefa kuri'ar ta raba gardama kan sabon daftarin kundin tsarin mulkin kasar.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh