′Yan adawar Kenya sun isa Kotu | Labarai | DW | 19.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawar Kenya sun isa Kotu

Jam'iyyun hamayya a kasar Kenya sun garzaya Kotu don kalubalantar zaben da ya baiwa shugaba Uhuru Kenyatta dama karo na biyu a zaben kasar.

Gamayyar jam'iyyun hamayya a kasar Kenya sun garzaya Kotu don kalubalantar zaben da ya baiwa shugaba Uhuru Kenyatta dama karo na biyu a zaben kasar da aka yi a ranar 8 ga wannan wata na Agusta. Madugun adawar kasar Raila Odinga wanda ya sami kashi 44 cikin darin kurin da aka kada a zaben, ya ki amince wa sakamakon da hukumar zabe ta bayyana, inda ta bai wa shugaba Kenyatta galaba da kuri'u sama da miliyan guda kan babban abokin hamayyarsa.

Batun kalubalantar zaben na Kenya dai, ya samu tushe ne bayan hukumar zaben kasar ta amince da wani yunkuri na yin kutse da bai yi nasara ba. Sai dai kungiyoyin sa ido na kasashen duniya da suka bi dddigin zaben, sun ce zabe ya gudana ba tare da wata matsala ba. Ana dai sa ran kotun kolin Kenyar, za ta yanke hukunci ne cikin makonni biyu da shigar da batun gabanta.