1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Harin Saudiyya a Yamen ya hallaka mayakan Huthi

Abdoulaye Mamane Amadou
October 11, 2021

Farmakin da dakarun kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kai a Yamen ya hallaka mayakan Huthi fiye da 150 a yankin Al-Abdiya da ke kudancin lardin Marib mai albarkacin man fetur.

https://p.dw.com/p/41Xrb
Jemen | Kämpfe in Marib
Hoto: AFPTV/AFP/Getty Images

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA, ya ce a sa'o'i 24 da suka gabata fiye da samame 30 dakarun kawancen suka kaddamar kan mayakan na Huthi, lamarin da kuma ya basu ansarar lalata motocin mayakan baya kisan wadanda suka kira da 'yan ta'adda. Daman dai ba kasafai mayakan na Hutsi ke bayyana adadin yawan mayakansu da ke mutuwa a fagen daga ba, a cewar wasu rahotanni. Rundunar sojan da ke yaki da mayakan dai ta kara zafafa kai hare-hare a baya bayan nan, lamarin da ya kara ta'azzara isar da kayayakin agaji ga fararen hula mabukata.