Yaki da al′adar auren wuri a Afirka | Zamantakewa | DW | 26.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yaki da al'adar auren wuri a Afirka

A karon farko 'yan siyasa da masu fafutuka da sarakunan gargajiya daga kasashe 27 da ke kan gaba wajen aurar da yara kanana sun gudanar da taron duba wannan lamari a kasar Senegal.

Shida daga cikin kasashe 10 da ke kan gaba wajen aurar da yara mata a duniya sun kasance a yankin yammaci da tsakiyar Afirka kan haka ne a karon farko 'yan siyasa da masu fafutuka da sarakunan gargajiya daga kasashe 27 suka gudanar da taron duba wannan lamari a birnin Dakar na kasar Senegal.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar a taron na birnin Dakar na nuni da cewar aurar da yara mata kanana da wuri na janyo wa kasashen yammaci da tsakiyar Afirka asarar kudi wajen dala biliyan 60. Kimanin yara mata miliyan 15 ne  wannan matsala ta auren wurin ke ritsawa da su a kowace shekara a duniya baki daya.

Bangladesch Kinderheirat (Getty Images/A. Joyce)

Auren wuri a Bangladesh

Daga cikin wannan kididdiga kasar Najeriya ce kan gaba sai Afirka ta Tsakiya da Chadi da Mali. Da ta ke jawabi a wurin taron kwararriya a fanin fafutukar kawo karshen wannan batu, Marie Christine Bocoum ta ce babbar illar aurar da yara da wuri ita ce yadda su ke ficewa daga makaranta ta kara da cewa a sabon yanayi da yara matan suka tsinci kansu, su kan fuskanci nau'oi daban daban na cin zarafi.

Darektan kungiyar kare hakkin yara Save the Children Eric Hazard, ya ce akwai munafurci cikin lamarin, domin ko a kasashe da ke cikin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ta kare 'yancin yara kanana, ana cigaba da al'adar aurar da yara kanana.

Bangladesch Kinderheirat (Getty Images/A. Joyce)

Auren wuri a kasar Indiya

Idan har aka tsayar da aurar da yara da wuri, ko shakka babu za'a samu raguwar haihuwa da wajen kashi 10 daga cikin 100. Hakan ba wai zai yi tasiri kan karuwar yawan jama'a kadai ba, amma har da inganta tattalin arzikin kasashen yankin, a cewar masanin tattalin arziki a babban bankin duniya Quentin Wodon, a jawabinsa a wurin taron.

Daura da matsalolin tattalin arziki da na cin zarafi a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya 'ya'ya matan da aka aurar da su da wuri kan rasa rayukansu ko kuma su kamu da cututtuka masu nasaba da karancin abinci mai gina jiki. A farkon watan Oktoba kasashen kungiyar tattalin arziki na yammacin Afirka 15 na ECOWAS, suka amince da dokar kare tare da goyon bayan yara mata kanana da ke fuskantar barazanar aure da wuri. Babban kalubalen yanzu  shi ne ganin hakan a aikace.

 

DW.COM