Nijar na bukatar dokar hana auren wuri | Siyasa | DW | 11.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar na bukatar dokar hana auren wuri

Gamayyar kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin mata da iyali, da hukumar UNICEF da UNFPE a birnin Yamai, sun shirya ganawa ta musamman da majalisar dokoki don nuna damuwa kan aurar da mata masu karancin shekaru.

Taron ya nuna tsananin bukatar gwamnati da majalisa su samar da doka ta musamman da za ta hana aurar da yarinyar da ke karatu da kuma wacce shekarunta basu kai 18 da hafuwa ba. Sai dai wannan yunkurin tuni ya fara shan suka daga bangarori daban-daban a fadin kasar. Wannan matsalar dai na a matsayin wani kashin gadon bayan tabarbarewar rayuwa da tarbiyar mata da 'yan mata a matsayin su na mafi girma daga rukunin jinsin al'ummar Nijar. Malam Abdou Mamane Lokoko, mamba ne a kungiyoyin Rosen mai fafatukar inganta ilimi a Nijar,  da ke cewa:

"Sai ka ga 'yan mata an barsu suna ta yawo suna talla, wasu kuma an masu fyade wasu kuma ana tozarta su, to abin haushi shi ne a makarantu wadanda suke cikin kamar malamai ko 'yan uwansu da ke yin cikin ba'a daukar wasu matakai."

Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger (DW)

Babban burin da gangamin ya ke son cimma shi ne ganin 'yan majalisar dokoki sun gamsu da matsalolin da a ke fuskanta, tare da samar da wata takamamiyar doka da zata haramta auratar da 'yan mata da ke karatu a makarantun boko ba tare da shekarun aurensu yakai ba. Malam Daouda Mamadou Marthe shi ne ministan Ilimin kananan makarantun bokon a jamhuriyar Nijar, wanda ya ke cewa:

"A cikin wannan shawarar da muka zo da ita, akwai malamai akwai sarakunan gargajiya akwai masana da 'yan farar hula bukatar shi ne kowa ya kawo shawara ta yanda zai sa a gobe idan muka kawo doka a nan a aminta da ita, kuma muna shirye shiryen yin doka da ke yaki da wannan."

Amma Laouali Maijirgi dan majalisar dokoki ne da ke ganin cewa " 'Yan mata kanana idan an hana su auren, an hana su daukar su a kaisu bakin ruwa.? inda yakin za'a yi da gaske da tun daga nan majalisa ka zo da dare ka gani yanda tun daga nan wajen tsintsiyar da kuka saka har Jado sekou yanda za ka ga yan mata kankana na yawon fasikanci a titi to mu uwayenmu sun shekara 18 ne kafin yi masu aure har su haifi shugaban kasa ?har ga allah ni ba zan sakawa dokar hannu ba."

Niger Pasto Suleimane Ibrahim und Ustaz Ashiru Malam Tukur in Maradi (DW/S. Kaka)

Fasto Suleimane Ibrahim da Ustaz Ashiru Malam Tukur a Maradi

Taron bitar ya tattaro shehunan Malamai da ke da akidar ta kyautata rayuwar 'yan mata da ke a makarantun boko, hada da sarakunan gargajiya da manazarta don wayar da kan 'yan majalisun dokoki a gabanin shigar da dokar da gwamnati ke son gabatarwa nan da wani dan lokaci.

Tsari dai na tare ne da tallafin hukumomin kasa da kasa kamar Unicef da Unfpe da sauran manyan kungiyoyi masu kare yara da iyali, lamarin da masu gaba da shirin ke kira wata takala ce da ke da nasaba da katsalandan a cikin iyali da gwamnatin ke son bijiorowa da ita.

 

Sauti da bidiyo akan labarin