UNICEF: Milyoyin yara mata kan fuskanci auren wuri | BATUTUWA | DW | 24.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

UNICEF: Milyoyin yara mata kan fuskanci auren wuri

Matsaloli masu yawa wadanda suka hada da cin zarafi zuwa ga samun asarar rai ake dangantawa da auren wuri ga yara mata masu kananan shekaru a wani lamari da ke kawo tarnaki ga ilimi da kuma uwa uba lafiyarsu.

 Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya kiyasta cewa yara mata kimanin miliyan 15 ake yi wa aure kafin su cika shekaru 18 da haihuwa, matsalar ta saka masu ruwa da tsaki akan batun shirya taro a birnin Dakar na kasar Senegal don gano hanyoyin shawo kan lamarin dake barazana ga rayuwar yara mata a sassan duniya. A cikin rahoton da kungiyar Save the Children mai kare hakkin yara ta fitar ya nuna a zahiri akwai dangantaka a tsakanin aurar da kananan yara mata, da matsalolin da ake samu na mata masu  juna biyu, gami da mutuwar yara jarirai, rahoton ya kara da cewa matsalar na kara kamari duk da cewa kasashe da dama sun amince da matakin haramta aure ga yara kanana inda aka kaiyade shekarun aure ya kasance daga shekaru 18 zuwa sama, a kasashe kamar Chadi da Malawi da Zimbabuwe da Costa Rica da kuma Guatemala sun kara yawan shekarun aure lamarin da ya saka aka samu nasara a zahiri.

US-Fotojournalistin Stephanie Sinclair

Rikice-rikicen yaki na haddasa matsalar auren wuri

Susanna Krüger ta shugabar kungiyar Save the Children reshen Jamus ta yi nazari kan batun inda take cewa akwai wasu dalilai na daban dake tilasta iyaye yi wa 'ya'yansu mata masu kanana shekarun aure."Iyaye ba sa aurar da yaran haka kawai amman misali idan aka samu yanayi na rikice-rikice ko kuma yake-yake, akwai maganar ba da kariya abin da ke janyo iyaye na aurar da yaransu mata."

Safarar mutane da ya karu daga milyan 11.3 zuwa milyan 11.5 tun shekara ta 2015 na cikin abubuwa da suka kara wannan matsala, kana akwai kimanin yara mata milyan Tamanin da biyu  wadanda suke tsakanin shekaru goma zuwa sha bakwai wadanda ba su da wata kariya ta shari'a yayin da wasu kimanin milyan casa'in da shida ke rayuwa cikin yanayi na rashin tabbas na gamuwa da auren wuri a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ko arewacin Afirka, da kasashen kudancin Asiya da kuma yammaci da tsakiyar Afirka.

Susanna Krüger ta Save the Children tana ganin duba matsalar daga tushe shi ne abin da ya dace domin samun mafita, ta tabo batutuwa da suka kunshi addini da al'adu da kuma talauci da rikice-rikice a matsayin tarnaki ga kokarin dakile tsarin aurar da kananan yara mata.Krüger tana ganin matakan siyasa da tabbatar da aiwatarwa za su taimaka gaya wajen magance matsalar, zaman taron na kasar Senegal zai mayar da hankali kan hanyoyin dakile matsalar kamar yadda tanade-tanaden Majalisar Dinkin Duniya na muradun karni suka shata.

Sauti da bidiyo akan labarin