Yaduwar cutar kyandar biri a Najeriya | Labarai | DW | 10.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaduwar cutar kyandar biri a Najeriya

Hukumomin kiwon lafiya a Najeriya sun bayyana fargabar yiwuwar cutar kyandar biri ta bazu a kasar, bayan da aka gano wasu gwamman mutane da ake zargi sun harbu da cutar a cikin jihohi bakwai na kasar.

Hukumar kula da cututuka masu yaduwa a kasar ta NCDC ta ce tun bayan mutuman farko da aka bayyana kamuwarsa da cutar a ranar 22 ga watan Satumban da ya gabata a cikin jihar Bayelsa ta Kudu Maso Gabashin kasar an samu ya zuwa yanzu mutane 31 da ake zargin sun kamu da cutar kyandar birin.

 Kuma yanzu ana fargabar yaduwar ta a jihohin Lagos birnin da ke kunshe da mutane miliyan 20. Daraktan hukumar ta NCDC Chikwe Ihekweazu ya sanar da cewa yanzu haka ana can ana gudanar da bincike kan wadanda ake zargin sun kamu da cutar. 

Sai dai kuma ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu, domin kuwa ya zuwa yanzu babu tabbacin cewa mutanen sun kamu ne da wanann cuta. A watan Satumba cutar ta kyandar biri ta halaka mutane 10 a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.