Yadda ′yan Najeriya ke kallon shugabancin Trump | Siyasa | DW | 19.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yadda 'yan Najeriya ke kallon shugabancin Trump

A daidai lokacin da Donald Trump ke cika shekara guda da hawa kan mulkin Amirka, abubuwa na bazata da ya yi a game da kasashen Afrika da ma Najeriya na zama abin da ke daukar hankali.

Shekara guda da shugaban Amirka na Donald Trump ya yi a kan karagar mulki ya kasance shugaban da ya fi fuskantar cece-kuce a game da manufofinsa. Domin duk abubuwan da aka yi hasashen za su faru saboda manufofi da halayensu na mazari ba a san gabanka ba, suke ta faruwa a cikin Amirkan da ma kasashen ketare.

Muhimmai da suka kasance na bazata su ne na fitar da Amirka daga muhimman kungiyoyin duniya, da janye ta daga batun rage dumamar yanayi, uwa uba batun takaita baki da kai tsaye ya shafi 'yan kasashen Afirka irin na Najeriya.

Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa ne da ke jami'ar Abuja ya bayyana yadda yake kallon shekara guda ta Donald Trump a matsayin shugaban Amirka.

"Zuwa yanzu Donald Trump bai ba marada kunya ba. Shekara guda da hawansa kan mulki bai nuna niyar yin abubuwan da magabatansa suka yi ba. Duk da babatu da yake yi game da kasashen Afirka da kuma bakaken fata zai iya yin abubuwa da magabantansa ba su yi ba. A fili take cewa nan gaba Amirka za ta yi wuyar shiga ga 'yan Najeriya da 'yan Afirka da Asiyawa."

Najeriya ta samu karbuwa wajen Trump

Duk da irin abubuwan da suke faruwa an ga Najeriya a matsayin kasar Afirkan da ta samu tagomashi wajen shugaban Amirka ta hanyar makaman da ya sayar mata don yakar masu aiyyukan ta'adanci.

Muhammadu Buhari speaks during an interview with Reuters at a private residence in Lagos, Nigeria (Reuters/A.Akinleye)

Najeriya ta samu karbuwa wajen shugaban na Amirka dangane da cinikin makamai

Shin yaya 'yan siyasa ke kallon wannan a daidai lokacin da shugaba Trump ke fursta kalamai na batanci? Mai Mala Buni fitaccen dan isyasa ne kuma sakataren jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

"Mu ba gwamnatin Trump muke kallo ba, mun fi karkata ga na mu shugaban Muhammadu Buhari. Ba wani shugaban Amirka ko ma ba Trump ba a halin da ake ciki yanzu ya ce zai juya wa Najeriya baya."

Amirka dai babbar kawar Najeriya ce a fannin kasuwanci, abinda ya sanya tun a 2008 Amirka ta bullo da tsarin karfafa cinikaiyya da kasashen Afirka irin na Najeriya, shirin da aka kara wa'adinsa sau biyu zuwa 2025. Ko a shekara guda na mulkin Trumph an ga wani sauyi a wannan fanni? Malam Adamu Garba dan kasuwa ne na kasa da kasa kuma dan siyasa.

"Mu 'yan Najeriya mu membobi ne na North Atlantic Alliance, ran da tekun Atlantika ya kare rannan muka kare, shi ya sa abin da na sani ba shi ne abin da muka karu da shi sai wanda muka ragu da shi."

A yayin da shugaba Donald Trumph ke cika shekara guda da mulkin Amirka, kasashe irin na Najeriya na nazari a tsanake don ganin matakin da mazarin zai dauka ko za a iya sanin gabansa.

Sauti da bidiyo akan labarin