Yadda omicron ke kokarin raba kawunan duniya | Siyasa | DW | 30.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yadda omicron ke kokarin raba kawunan duniya

Gwamnatoci a sassan duniya sun kaddamar da tsauraran matakai na takaita tafiye-tafiye daga yankin Kudancin Afirka inda sabon nau'in cutar corona ta fara baiyana.

Kwatsam aka wayi gari da labarin bullar wani nau'in corona mai suna Omicron wanda kwararru a fannin lafiya suka ce yana da hadarin gaske. Kasashen duniya na cikin zulumi dangane da annobar corona da ke ci gaba da rikida zuwa nau'uka a daidai lokacin da cutar ta fara mamayar duniya a karo na hudu.

A wani mataki na takaita yaduwar sabon nau'in cutar, gwamnatoci a sassan duniya sun kaddamar da tsauraran matakai na takaita tafiye-tafiye daga yankin Kudancin Afirka inda sabon na'uin cutar corona ta fara baiyana, matakin da Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce babu hujjar hakan ko a kimiyyance. 

Deutschland | G20 | Compact with Africa meeting in Berlin | Cyril Ramaphosa

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu

"Muna kira ga wadannan kasashe da suka kafa dokar hana tafiya a kan kasashenmu na yankin kudancin Afirka da su gaggauta sokewa, kafin su kara yi mana wata illar akan tattalin arzikinmu da rayuwar al'ummarmu"

Karin Bayani: 

Har yanzu, masana kimiyyan ba su gano hadarin yadda omicron ke yaduwa tsakanin mutane ba, balle sanin ko allurar riga-kafin da ake yi za ta cigaba da yin tasiri, kamar yadda Leif Erik Sander na asibitin Charite da ke Berlin ya nunar...

"Har yanzu babu cikakken sakamakon bincike na kimiyya, amma ana cikin yinsa a dukkan fadin duniya domin ganin martanin garkuwar jiki da tasirin allurar rigakafin ko kuma akasin haka. Wajibi ne muyi hakuri yayin da bincike ke gudana. Yin allurar ta uku na da muhimmanci, musamman da bayyanan sabbin nau'oin cutar. Allurar na da kariya"

Deutschland Berlin | Sitzung Bundestag | Angela Merkel

Jamus na cikin wadi na tsaka mai wuya

Tuni Jamus ta fada cikin wadi na tsaka mai wuya, a wani abun da ke zama mafi munin yaduwar corona a tarihin annobar. Sai ga shi kuma matafiya daga Afirka ta Kudu sun shigo kasar da omicron, batu da ke kara barazana ga tsarin lafiyarta a cewar ministan lafiya Jens Spahn...

 "A yanzu haka jiragen sojin sama na cigaba da jigilar marasa lafiya daga wannan asibitoci zuwa wata a nan Jamus. Wannan ai abun mamaki ne a tarihin Jamus. Ina fatan wannan kadai ya zama izna ga mutane da dama da ke adawa da riga-kafin da su sauya tunani, saboda muhimmancinta" Karin Bayani: Jamus: Fargabar barkewar corona karo na hudu

Ko shakka babu Isra'ila ta ji wannan kiran. Da samun mutane biyu da ke dauke da nau'in Omicron da kuma wasu da ake zargin sun kamu, tuni ta rufe dukkan kan iyakar kasar ga matafiya daga ketare na tsawon makonni biyu, inda ake amfani da fasahar zamani da wayoyin sirri na bin diddigin mutane da suka kamu. Matakin da ke zama tsaurara kuma cikin gaggawa da mahukuntan kasar ta Baniyadu ta dauka, tun bayan bullar sabon nau'in corona wato omicron. 

Malaysia Covid-19 Pandemie Maßnahmen Impfung

An ga tasirin allurar riga-kafin corona

Ita ma Japan ta sanar da hadewa da Isra'ilar wajen rufe kan iyakokinta ga masu shigowa daga ketare, domin kare yaduwar omicron, inda ta sanya matakai mafi tsauri tun bayan bullar wannan nau'i na cuta a yankin kudancin Afirka. Firaminista Fumio Kishida ya ce, matakan na wucin gadi ne, har ya zuwa lokacin da za a samu cikakkun bayanai dangane da wannan sabuwar barazanar a kokarin da duniya take yi na kawar da annobar coronavirus da ta yi wa duniya zobe tun shekaru biyu da suka gabata.

Sauti da bidiyo akan labarin