1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan Omicron

Zainab Mohammed Abubakar
November 29, 2021

Ministocin lafiya na kasashe masu mafi karfin tattalin arziki za su yi taron gaggawa a kan sabon nau'in cutar corona na Omicron mai saurin yaduwa tsakanin mutane.

https://p.dw.com/p/43bYS
G7 - Gipfeltreffen der Gesundheitsminister, Oxford University
Hoto: Stefan Rousseau/empics/picture alliance

Matakin da ke zuwa a dai dai lokacin da kwararru a fannin lafiya ke kokarin fahimtar me sabon nau'in ke nufi ga fafutukar da ake yi na kawar da wannan annoba da ke neman zama gagarabadau.

Shugabar kungiyar G7 ta yanzu watau Birtaniya, ita ce ta kira taron na wannan Litinin, kasar da ke zama daya daga cikin wadanda ya zuwa yanzu sanon nau'in Omicron din ya iso cikinta.

Omicron da aka fara ganowa a kasar Afirka ta Kudu, na zaman wani babban sabon kalubale ne a yaki da annobar COVID 19. Tuni dai wasu kasashe suka sake daukar tsauraran matakai game da tafiye tafiye.