1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Omicron: Japan ta hana matafiya shiga kasarta

November 29, 2021

Bayan sassauta wasu dokokin shiga kasar, Japan ta sake hana matafiya daga kasashen waje shiga kasarta da nufin dakile yaduwar sabon na'in cutar Corona mai suna Omicron a kasar.

https://p.dw.com/p/43cWU
Japan schließt wegen Omikron-Variante erneut Grenzen für Ausländer
Hoto: Koji Sasahara/AP/picture alliance

Firanministan kasar Fumio Kashida ya baiyana cewa dokar zata fara aiki ne a ranar Talata. Ana dai ganin bullar sabon nau'in cutar ya kawo cikas ga dokokin da kasar ta sassauta a farkon wannan watan da ya bai wa dalibai da 'yan kasuwa damar shiga kasar.  

A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta nuna damuwarta kan hatsarin sabon nau'in cutar coronar wadda aka fara ganota a kasar Afirka ta Kudu, inda kuma ta bulla a kasashen Kudancin nahiyar Afirka da Turai da kuma Asiya.