Wulff na ziyarar Turkiyya | Siyasa | DW | 19.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wulff na ziyarar Turkiyya

Mutane sun ɗokata domin jin jawabin shugaban ƙasar Jamus Christian Wulff gaban majalisar dokokin Turkiyya.

default

Christian Wulff na Jamus da takwaransa Abdullah Gül na Turkiyya

Ziyarar ta shugaban ƙasar Jamus Christian Wulff ta fara ne da tuntuɓar juna a birnin Ankara, fadar mulkin ƙasar Turkiyya. Bayan ajiye furanni a kushewar uban ƙasa Kemal Atatürk. Christian Wull ya gana ido huɗu da takwaransa shugaban ƙasar Turkiyya Abdallah Gül kuma ba'ada bayan haka ya sadu da piraminista Tayyib Erdowan. Kuma ko da yake a halin da ake ciki yanzu maganar sajewar baƙi a Jamus ita ce ta mamaye manufofin cikin gida na ƙasar, amma shugaban ƙasa Christian Wulff yayi amfani da wannan ziyarar tasa domin bayyana ainihin alƙiblar da aka sa a gaba. A cikin wata hira da jaridar Hürriyet ta ƙasar Turkiyya tayi da shi sai da ya musunta iƙirarin da shugaban jam'iyyar Christian Social Union Horst Seehofer yayi na cewar 'yan kaka-gida daga Turkiyya da ƙasashen Larabawa na karantsaye ga fafutukar sajewa da Jamusawa. Wulff ya ce:"Babban kuskure ne a yi iƙirarin cewar wani rukuni na al'uma gaba ɗayanta na ƙyamar sajewa. Ina adawa da irin wannan iƙirarin na cewar dukkansu jirgi ɗaya ne ke ɗauke da su. Lamarin ya banbanta tsakanin ɗaiɗaikun mutane. Wajibi ne gwamnati da sauran al'umar ƙasa su taimaka wajen ba da damar sajewar. Sannan su kuma a na su ɓangaren wajibi ne ɗaiɗaikun mutane su yi amfani da wannan dama."

Kazalika dangane da maganar zaman Turkiyya cikakkiyar wakiliya a ƙungiyar tarayyar Turai, shugaban ƙasa Christian Wulff bai goyi bayan ra'ayin wasu 'yan Christian Union ba, inda ya bayyana irin amfanin dake tattare da irin wannan wakilci yana mai yin kira da shiga tattaunawa tsakani da Allah bisa manufa.

Bayan da a 'yan kwanaki da makonnin da suka wuce a can ƙasar Turkiyya ba a ba da la'akari da ɓaɓatun da ake yi game da maganar sajewar baƙi a nan Jamus ba, amma fa a karon farko a yau kafofin yaɗa labarai sun gabatar da cikakkun rahotanni akan matsalar. Wani masharhancin jaridar Miliyet, mai sassaucin ra'ayi dake fita kullu-yaumin a ƙasar Turkiya, Semih Idiz yayi nuni da cewar:

"A yau dai Jamus ta fito fili ta haƙiƙance cewar tana fama da wahala wajen karɓar musulmi da hannu biyu-biyu. Wannan shi ne halin da ake ciki a duk faɗin Turai yanzu haka. Haƙiƙancewa da hakan na da muhimmanci matuƙa ainun. Domin ita ma Turkiyya, kamar yadda aka sani, sai da ta sha fama da wahala kafin ta haƙiƙance da matsalarta ta Ƙurdawa. Amma babban abin tambaya a yanzu shi ne, mene ne zai biyo baya? Shin wani mataki Jamus zata ɗauka bisa manufa?

Indiz yayi kira da a ƙara ƙarfafa tuntuɓar juna tsakanin Jamus da Turkiyya, musamman akan wannan batu. Ana ma iya farawa tun yau sakamakon ziyarar shugaban ƙasar Jamus ga Turkiyya, in ji ɗan jaridar. Nan gaba a yau talata ne ake sa ran shugaban ƙasa Christian Wulff zai zama shugaban Jamus na farko da ya zai gabatar da jawabi ga majalisar dokokin Turkiyya. Ba shakka ana alla-alla a ji jawabin nasa, musamman ma dangane da buƙatar Turkiyya ta zama cikakkiyar wakiliya a ƙungiyar tarayyar Turai.

Mawallafi: Ulrich Pick/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu