WHO: Za a samu karuwar corona a watan azumi | Labarai | DW | 01.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO: Za a samu karuwar corona a watan azumi

Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO a yankin Gabas ta Tsakiya Ahmed al-Mandhari ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar a samu karuwar sabbin kamuwa da corona a lokacin azumin Ramadana da kuma lokacin bukukuwan Ista.

WHO ta ce tana sane da muhimmancin watan Ramadan da bukuwan Ista amma akwai bukatar kowa ya dauki matakin kare kansa daga cutar ta corona.

Tun kafin yanzu dai kasashen Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce sun dakatar da tarukan ciyar da mutane abinci a watan Ramadan. Sai dai sun ce za su amince a yi sallar Taraweeh amma sun takaita yin sallar ta Taraweehin ga mintuna 30 kadai.