WHO ta tabbatar da bullar kwalara a Kenya | Labarai | DW | 22.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO ta tabbatar da bullar kwalara a Kenya

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fito da wani gargadi kan alamun ta'asar cutar kwalara a kasar Kenya, sakamakon tabbatar da kasancewar kwayoyin cutar da ta yi.

Cikin wata sanarwar da ta yi dangane da lamarin, hukumar ta lafiya ta duniya ta ce ya zuwa yanzu ta tabbatar da kamuwar sama da mutum 300. Tuni ma dai cutar ta kwalara ta kashe mutane hudu a wasu manyan Otel-otel da ke Nairobi babban birnin kasar.

Hukumomin birnin sun dauki matakan bincike bayan samun akalla mutane 30 da suka kamu. An kuma fara tsananta binciken a wuraren saukar baki da kuma gidajen sayar da abinci. Ko a bara ma dai cutar ta kwalara ta kashe sama da mutane 200 a kasar yayin da wasu dubbai kuwa suka sha jinya.