Watanni 6 na Banda a kujerar mulkin Malawi | Siyasa | DW | 26.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Watanni 6 na Banda a kujerar mulkin Malawi

Joyce Banda ta kasance mace ta biyu da ta taɓa shugabantar wata ƙasa a Afrika, wadda aka rantsar da ita bayan mutuwar tsohon shugaba Bingu Wa Mutharika a watan Afrilu.

Da hawan ta karagar mulkin wannan ƙasa da ke yankin kudu maso gabashin Afrika watanni shida da suka gabata, ta yi alkawarin kawar da talauci tare da yin gyare-gyare dan gane da matsanacin talauci da ke addamar al'ummar ƙasar. Ko yaya dangantakar Malawi da tarayyar turai aƙarƙashin jagorancin Banda?

Hawanta karagar mulki ke da wuya Joyce Banda ta sanar da rage yawan albashinta, a matsayin Shugabar ƙasa. Suma ministocinta dole suka salwantar da kashi guda daga cikin uku na albashinsu. Wannan dai mataki ne da al'ummar Malawi suka yi maraba dashi, kasancewarta ɗaya daga cikin ƙasashe da talauci ya yi wa katutu a nahiyar Afrika.

Banda dai ta samu karɓuwa sosai a tsakanin ƙasashen turai da ke bawa Malawi taimakon raya ƙasa. Wanda hakan ba zai kasa nasaba da soke zama mai masaukin baƙi na taron ƙungiyar gamayyar Afrika, da aka tsara gudanarwa a Malawi ba a watan yuni, saboda AU ta jajirce cewar sai shugaba Hassan Omar al-Bashir na Sudan ya halarci taron, mutumin da kotun ƙasa da ƙasa mai shari'ar miyagun laifuka ta ICC ke nema ruwa a jallo.

Fisch ist für die Malawier die wichtigste Eiweißquelle. Männer sitzen auf ihre Boote am Strand. Copyright: DW/Mathias Bölinger Oktober, 2010, Malawi

Sana'ar Su

Dangantaka da Nahiyar Turai

Dangantaka tsakanin tsohon shugaban Malawi, marigayi Bingu Wa Mutharika da Amurka da turai dai tayi tsami, inda ya ce su kai tallafin da suke wa ƙasarsa kasuwa, baya buƙata. Sakamakon hakan dai malawi ta fuskanci matsananci yanayi na durƙushewar tattalin arziki. Bayan mutuwarsa a watan Afrilun shekara ta 2012 ne aka rantasar da mataimakiyarsa Joyce Banda domin maye gurbinsa, kamar yadda kundun tsarin mulkin ƙasar ya tanadar.

A cewar Christiane Bertels-Heering ta ƙungiyar dangantakar Jamus da Malawi, sabuwar shugabar ba wai kawai ta cimma samarwa da ƙasar sabon tallafi daga ketare ba ne, har ma da ɗora Malawi akan sabuwar alkibla.

Ta ce " akwai ƙananan masana'antun harkokin noma da ke muradin sake haɗewa domin aiki tare. Akwai tambayoyi da yawa dangane da keken ɗinki. Saboda Mata na samun ranchen kuɗade na gudar da sanao'i daga banki. Suna iya sayen kekunan ɗinki, domin yin kayayyakin da zasu iya sayerwa domin samun sukunin biyan kuɗaɗen da suka karɓa rance daga Banki. Kana su ci gaba da amfani da kekunan ɗinkin akan wasu ayyuka domin inganta rayuwarsu".

A ganin Bertels Heering dai salon tsarin siyasar Banda dai sannu a hankali zai iya sake farfaɗo da tattalin arzikin Malawi. Duk kuwa da cewar rayuwar wasu 'yan Malawin na cigaba da lalacewa. Akwai wahalhalu na ƙarancin abinci, ga jerin gwanon motoci a wuraren sayar da Mai da iskar gas, a yayin da farashin kayayyakin masarufi sai daɗa hauhawa yake yi.

Bunkasar tattalin arziki

Manazarta kamar sakataren ƙungiyar gamayyar kasuwancin Jamus a kudancin Afrika, Andreas Wenzel na zargin shugabar Malawin da wannan hali da ƙasar ke ciki bisa la'akari da tsananta ka'idojin hukumar bada lamuni ta Majalisar Ɗunkin Duni watau IMF.

Yace " musamman dan gane da rage darajar kuɗi da ma kaɗaɗen shiga na ƙasar. Ga yajin aiki da tashe tashen hankula, wanda ke gwajin bukatar shugabar ta daidaita lamuranta na mulki. Dole ne ta tabbatarwa da Al'ummar Malawi cewar, waɗannan matakan nada nufin tsamo ƙasar daga kura-kuren marigayi shugaba Bingu Wa Mutharika".

Watanni shida bayan hawa karagar mulkin Joyce Banda dai, 'yan Malawi sun ce basu gani a ƙasa ba dangane da bunkasar tattalin da tayi alkawari. Ko da yake ƙasar na iya cin moriyar bunkasar tattalin ƙasashe makwabta kamar Mosambik.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal