Wata ′yar kunar bakin wake ta tarwatse a Kano. | Labarai | DW | 28.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata 'yar kunar bakin wake ta tarwatse a Kano.

An sake kai harin kunar bakin wake a Kano, inda wata mata cikin hijabi dauke da bam ta tarwatse a tsakiyar jama'a, a wani gidan mai da ke Hotoro.

Rahotanni daga birnin Kano na Najeriya sun ce, a kalla mutane 3 ne suka rasu, wasu kuma da dama suka jikkata lokacin da wata 'yar kunar bakin wake ta tashi bam din da ke jikinta a babban gidan man NNPC da ake kira Mega station da ke unguwar Hotoro. Shaidun gani da ido sun bayyana cewar wata mata ce dai ta zo da bam din boye a cikin kayan ta, inda tayi kokarin kutsawa cikin daruruwan mutanen da suka yi layi domin sayen kalanzir, inda kan injin da ake bada kalanzir din ya kama da wuta, haka kuma mutane da dama sun konkone tare da samun raunuka.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Abubakar Labaran Yusif da ya halarci asibitin Murtala inda ake kula da wadanda suka jikkata, ya tabbatar da cewa a kalla mutane bakoye ne suka jikkata sakamakon harin. A jiya Lahadi ma dai (27.07.2014) mutane biyar sun rasu, a wani harin da aka kai ga wani Cocin Katholika a birnin na Kano, sannan kuma wata yar kunar bakin wake a jiyan tayi sanadiyar raunana 'yan sanda a kalla biyar kusa da wata Jami'ar birnin na Kano.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar