1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Wata fashewa ta kashe mutum biyu a Rasha

February 17, 2026

Har zuwa yanzu ba san musabbabin fashewar da ta auku a sansanin sojojin na Rasha ba, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

https://p.dw.com/p/58uZf
Jami'an tsaron Rasha suna killace wani wuri da aka samu fashewar abubuwa a 2025
Jami'an tsaron Rasha suna killace wani wuri da aka samu fashewar abubuwa a 2025Hoto: Ramil Sitdikov/REUTERS

Mutum biyu sun mutu sakamakon wata fashewa da ta auku a wani sansanin soji a garin Sertolovo da ke yankin Leningrad na Rasha.

 Wata tasha mai suna Mash a Telegram ce ta ruwaito faruwar lamarin dazu-dazunnan kamar yadda hukumomi da kansu suka tabbatar.

Putin ya ce Rasha za ta cimma muradanta na yakar Ukraine

Gwamnan yankin, Alexander Drozdenko, ya ce fashewar ta faru ne a cikin wani ginin soja, sai dai bai bayar da karin bayani ba.

Ya ce, ya umarci jami’an tsaro su taimaka wa sojoji wajen kwashe baraguzai da ceto wadanda suka jikkata sakamakon rushewar ginin sojin a Sertolovo.

Rasha ta kai munanan hare-hare a kudancin Ukraine

Tashar Mash ta Telegram ta kuma ruwaito cewa ana kyautata zaton mutum hudu na iya kasancewa a ƙarƙashin baraguzan ginin.