Wata fashewa ta hallaka mutane 10 a Bauchi | Labarai | DW | 28.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata fashewa ta hallaka mutane 10 a Bauchi

Tashe-tashen bama-bamai na ci gaba da kassara lamura a yankin arewacin Najeriya

A Tarayyar Najeriya, rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi ta bakin kakakinta DSP Haruna Muhammad ta tabbatar da rasuwar mutane goma, yayin da 14 suka samu munanan raunuka, sanadiyar fashewar wani bam a wani hotel da ake kira People's Hotel da ke wata unguwa da ake kira unguwar bayan-gari cikin garin Bauchi a arewacin Najeriya.

Wakilinmu da ke Bauchi Ardo Abdullahi Hazzad, ya ce fashewar bam din ta zo dai dai lokacin da al'ummar Musulmi ke jiran ace an ga watan Ramadan, wanda da dama daga ciki sun zaci karan bindiga ce ta ganin watan, wanda aka ce an gani a wasu arewacin Tarayyar ta Najeriya. Rundunar 'yan sandan ta ce za ta yi cikakken bayani bayan bincike a safiyar yau Asabar.

Mawallafi: Ardo Abdullahi Hazzad
Edita: Suleiman Babayo