Wasu sojojin Rasha 18 sun mutu a OMSK | Labarai | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu sojojin Rasha 18 sun mutu a OMSK

Sojojin sun mutu bayan faɗuwar ginin wata rundunar sojojin a OMSK da ke a yankin Siberiya

Majiyoyi daga ofishin ministan tsaro na ƙasar Rasha sun ce wasu sojoji guda 18 na ƙasar sun mutu bayan da wani ginin wata rundunar sojojin da ke kusa da OMSK da ke a Siberiya ya rikito a daran jiya Lahadi zuwa yau Litinin.

Yanzu haka dai ofishin minitan tsaro na ƙasar ta Rasha ya ce ana neman wasu sojoji guda biyar waɗanda ya ce sun yi ɓatan dabo bayan haɗarin a rundunar ta sojojin leima da ke a gabashin ƙasar.

Kana an kwantar da wasu guda 19 a asibiti ana jinyanrsu. A halin da ake ciki dai hukumomin tsaro na Rasha ba su bayyana dalilan faruwar haɗarin ba.