Wasannin Olympic na lokacin kankara | Zamantakewa | DW | 22.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wasannin Olympic na lokacin kankara

A ranakkun 9 zuwa 25 ga watan Febrairun sabuwar shekara ta 2018 ne dai Koriya ta Kudu za ta dauki nauyin gudanar da wasannin Olympic, Rasha ta ce ba za ta nuna wasannin ba.

Kafofin yada labaran kasar Rasha sun yi kashedin cewar ba zasu nuna wasannin a gidajen talabijin dinsu ba, matsawar dai aka haramta wa 'yan wasan kasar ta Rasha halarta a bisa dalilin binciken amfani da kwayoyin kara kuzari.

A farkon watan Disamba mai zuwa ne dai hukumar kula a wasannin na Olympic za ta bayyana matsayinta a kan batun badakalar shan kwayoyin masu kara kuzari da aka zargin 'yan wasan kasar Rashar sun yi amfani da su