1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Gasar cin kofin Afirka AFCON 2021

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 10, 2022

Mai masaukin baki Kamaru ta lallasa Burkina Faso a wasan farko na gasar cin kofin kwallon kafar Afirka AFCON. Borussia Dortmund ta rage tazarar da ke tsakaninta da Bayern Munich a teburin Bundesliga.

https://p.dw.com/p/45MC8
Fußball Africa Cup of Nations
Hoto: Gavin Barker/Sports Inc/empics/picture alliance

A karon farko cikin tarihin gasar cin kofin Afrikan dai, masu horas da 'yan wasa 15 cikin 24 sun fito daga nahiyar. Daga cikin su akwai tsofaffin 'yan wasa da suka yi suna da wasu masu horaswa na kasashen Afirka da ke neman yin suna ga misali mai horas da 'yan wasan Senegal Aliou Cissé ya kasance tsohon dan wasan baya mai farin jini, kuma ya yi nasarar sauya sheka zuwa horaswa.

Tun bayan da ya karbi ragamar horas da 'yan wasan Senegal a 2015, ya jagoranci kungiyar Lions zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018 da kuma zuwa wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2019, inda ta sha kashi a hannun Aljeriya. Shi ma Mondher Kebaier na Tunisiya tsohon dan wasa ne a kungiyar CA Bizertin. A shekarar 2019 ne aka nada Kebaier a matsayin mai horas da 'yan wasan Tunusiya. Har yanzu dai kungiyarsa na ci gaba da neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar, amma za ta fara kokarin lashe gasar cin kofin Afrika karo na biyu bayan gasar da ta lashe a shekara ta 2004.

Gasar cin kofin Afirka AFCON | Karawar Senegal da Zimbabuwe
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Najeriya na daga cikin kasashen Afirka da suke da mai horas da 'yan wasa 'yan kasa, domin kuwa Augustine Eguavoen ya maye gurbin Gernot Rohr na Jamus, a matsayin mai horas da 'yan wasan kasar. Amma Augustine Eguavoen ya san Super Eagles sosai. Wannan dai shi ne karo na uku da tsohon dan wasan na Najeriya wanda ya buga wasanni 49 tare da cin kwallo daya ya samu kansa a matsayin mai horas da 'yan wasan na Najeriya. Dole ne tsohon mai tsaron baya ya nuna kwarewa da jajircewa don kai Super Eagles gaba gwargwadon iko a wasan na AFCON.

Harkokin kasuwanci na cikin abubuwan da suka bunkasa sakamakon zuwan baki daga kasashen ketere kuma Suleiman Babayo ya yi mana nazari kan batun na kasuwanci.

Tuni aka fara fafatawa a gasar ta AFCON kuma Kamaru mai masaukin baki da yi nasara a wasan da ta a yayin bude gasar. G

Gasar cin kofin Afrika| Ethiopia da Verde
Hoto: Ulrik Pedersen/NurPhoto/picture alliance

Har yanzu dai muna kan gasar ta AFCON, inda kasar Habasha da ke fama da rikici na sama da shekaara guda ke cikin kasashen da za su barje gumi a wasannin na AFCON kuma tuni ma ta yi wasanta guda daya. Koda yake Habashan ta sha kashi a hannun Cape Verde da ci 1-0 mai ban haushi.

Jamus| Gasar Bundesliga | A lokacin da Robert Lewandowski ya ci kwallo
Hoto: Ulrich Hufnagel/Imago Images

Idan muka dawo nahiyar Turai kuwa, a karshen mako aka dawo wasannin kakar Bundesliga ta bana bayan hutun sanyin hunturu na makonni biyu. A karshen ranar Jumma'ar da ta gabata dai, Bayern Munich da ke saman tebur, ta sha kashi a hannun Borussia Mönschengladbach da ci 2-1. A ranar Asabar kuwa an tashi wasa canjaras 2-2 tsakanin Bayer 04 Leverkusen da FC Unioin Berlin, haka ma abin yake a wasan da aka fafata tsakanin Freiburg da Armenia Bielefeld, inda su ma suka tashi canjaras 2-2. A wasan da Fürth da Stuttgart suka buga kuwa sun tasahi tashi 0-0 a tsakaninsu. Ita kuawa RB Leipzig ta yi wa  Mainz cin kaca da ci 4-1, kana an tashi wasa Hoffenheim na da ci uku Augsburg na da ci daya. Bochum ta lallasa Wolfsburg da ci daya mai ban haushi, Cologne kuma ta caskara Herther Berlin da ci 3-1. Ita kuwa Borussia Dortmund ta yi abin kai ne, inda ta samu damar rage gibin da ke tsakaninta da Bayern ta hanyar lallasa Eintracht Frankfurt da ci 3-2. Har yanzu dai Bayern din ce ke saman tebur da maki 43 yayin da Borussia Dortmund din ke biye mata a matsayi na biyu da maki 37 sai kuma Hoffenheim a matsayi na uku da maki 31 kana Freiburg ta koma matsayi na hudu da maki 30.

Ostraliya| Zanga zangar magoya bayan dan wasan Tennis Novak Djokovic
Hoto: Hamish Blair/AP/picture alliance

Magoya bayan shararren dan wasan Tennis na duniya Novak Djokovic sun yi ta tsallen murna a harabar kotu a kasar Ostiraliya, bayan da alkali mai shari'a Anthony Kelly ke mayar masa da takardar izinin shiga kasar wato visa. Alkali Kelly dai ya bai wa mahkuntan na Ostiraliya umarnin sakin Djokovic daga killace shin da aka yi a otel cikin mintuna 30 da yanke hukuncin. Sai dai lauyan gwamnati ya sanar da cewa, ministan lura da al'amuran da suka shafi bakin haure da 'yan ci-rani da kuma zama dan kasa da al'adu zai yi nazarin hukuncin ya kuma bayar da sakamko. Wannan dai na nuni da cewa har yanzu akwai yiwuwar a mayar da Djokovic gida wanda hakan ke nufin ba zai fafata a babbar gasar tennis ta Australian Open da za a fara a ranar 17 ga wannan wata na Janairu ba. Tun da fari dai gwamnatin Ostiraliyan ta soke takardar izinin shiga kasarta wato visa da aka bai wa Djokovic mai shekaru 34 a duniya jim kadan bayan isarsa kasar inda ta ce bai cika sharudan kebewa daga bin ka'idojin corona da aka gindaya wa baki da ke shiga kasar ba. Takardun kotu dai sun nunar da cewa Djokovic bai yi riga-kafin corona ba, sai dai kuma ba shi da bukatar yin allurar kasancewar ya kamu da annobar ya kuma warke a watan Disamba.