1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani ya yi yunkurin kona majami'a a Amirka

April 18, 2019

Kwanaki kalilan bayan konewar majami'ar Notre Dame mai dumbin tarihi a Faransa, jami'an tsaro a birnin New York na Amirka, sun kama wani da ya kutsa majami'ar St. Patrick.

https://p.dw.com/p/3H0KJ
Papst Franziskus in der St. Patrick Kathedrale in New York
Hoto: Getty Images/Chad Rachman

Mutumin mai shekaru 37 wanda har yanzu ba a bayyana asalinsa ba, ya fito ne daga wata motar da ya tsayar a harabar majami'ar dauke da man fetur da kayan hada wuta.

Masu gadi ne dai suka dakatar da shi, bayan gaza gamsar da su niyyarsa ta shiga da fetur din da ma kayan hada wutan. 

Daga nan ne suka yi gaggawar sanar da jami'an 'yan sandar yaki da ta'addanci a birnin na New York, wadanda da ma ke kusa da wajen.

An kuma kama shi ne da galan hudu na man fetur da kuma wasu sinadaran, baya ga wasu abubuwa na hada wuta.