Wani makeken dutse ya wuce kusa da wannan duniya
February 16, 2013Talla
Wani makeken dutse wanda girmarsa ya kai na filin kwallon kafa ya wuce kusa da duniyar da mu ke ciki da nisan kilo-mita 27,000.
Wannan ya zama kusanci sosai, saboda kusancin ya fi na taurarun dan Adam da su ke taimakawa harkokin sadarwa a duniya.
Tun da farko wata tauraruwa mai wutsiya da ta tarwatse ta jikata daruruwa mutane a kasar Rasha.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas