Wani Jirgin kasar Iran ya yi hatsari | Labarai | DW | 18.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani Jirgin kasar Iran ya yi hatsari

Wani jirgin saman fasinja na kasar Iran ya fadi a wani yanki da ke kudu maso yammacin kasar, inda ake fargabar fasinjoji 60 da masu hidima shida sun salwanta.

Jirgin mallakin kamfanin Aseman Airlines ya fadi ne cikin wasu tsaunukan Dena da ke kusa da birnin Semirom a wannan Lahadin. Kakakin kamfanin na Aseman, ya ce dama jirgin ya bar birnin Tehran ne kan hanyarsa ta zuwa Yasuj, ba akuma kaiga tabbatar da musabbabin hadarin ba. Jiragen kamfanin dai na daga cikin jiragen da hukumar kasashen Turai ta ce kasada ce shigarsu, saboda tsufa. Hatsarin jirgin sama na baya a Iran din dai shi ne na watan Agustan shekara ta 2014, inda mutane 37 suka halaka.