Wani abu mai kama da bam ya tashi a Jimet a Najeriya | Labarai | DW | 25.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani abu mai kama da bam ya tashi a Jimet a Najeriya

Rahotanni da ke fitowa da birnin Jimeta na jihar Adamawa sun ce wani abu mai kama da bam ya tarwatse a ofishin 'yan sanda da ke kusa da wasu makarantun firamare.

Ana fargaban cewa lamarin na iya shafar rayuka musamman na ‘yan sandan da ke bakin aiki inda abin da ake zato bam ne ya tashi ne a wata ma'ajiyar nakiyoyi da ke ofishin, wanda ke makwabtaka da makarantun firamare akalla biyu da kuma gidan yari, sannan da kotu da ma wasu ma'aikatu na gwamnati. Wani da ya shaida lamarin da idanunsa ya bayyana wa wakilinmu na Adamawa Muntaqa Ahiwa cewar sun ga yadda rufin kwanon ofishin ya tarwatse baki daya, kuma sun ga wasu abubuwa da ke kama da naman mutane da suka ciccire.

Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga jamai'an 'yan sanda dangane da wannan batun wanda ya harzuka jama'a musamman iyayen yaran da ke cikin makarantu na kusa da wannan waje.