1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Me ke wakana a Olympics ta birnin Tokyo?

Mouhamadou Awal Balarabe AMA
August 2, 2021

A daidai lokacin da aka shiga mako na biyu na gasar Olympics 'yan guje-guje da tsalle-tsalle na Najeriya na ci gaba da kaurin suna a fannin amfani da magungunan kara kuzari.

https://p.dw.com/p/3yRJR
Tokio 2020 | Leichtathletik
Hoto: Martin Meissner/dpa/AP/picture alliance

Dan damben boxing na kasar Ghana Samuel Takyi ya cancanci zuwa wasan kusa da na karshe na gasar olympics na kasar Japan, bayan da ya doke dan kaar Columbia David Avila da turmi uku da biyu. Wannan nasarar ta tabbatar wa Takye samun lashe akalla lambar tagulla saboda babu wani was samun matsayi na uku a damben Olympic. Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 29 da Ghana za ta lashe lambar Olympics tun bayan wasannin Barcelona a shekarar 1992. A gobe Talata ne dan damben Ghanan mai shekaru 20 Samuel Takyi zai yi gwajin kwanji da dan damben  Amirka Duke Ragan da nufin samun matsayi a wasan karshe.

A kokawar zamani 'yan Afirka ba su taka rawar gani ba
Babu dan dambe ko daya da ya tsallake zagayen farko ciki kuwa har da Abdelkarim Fergat na Aljeriya da Haytem Mahmoud na Masar a 'yan kasa da kilo 60. Haka shi ma dan Tunisiya Amine Guennichi da Abdellatif Mohamed' na Masar a ajin nauyin kilogram 130 ba su kai labari ba. A rukunin mata ma 'yar Tunisiya Zaineb Sghaier da Samar Amer Ibrahim Hamza ta Masar a wasan kokawa na' yan kasa da kilo 76 sun dibi kashinsu a hannu. Sai dai a rukunin 'yan kasa da kilogram 68 na mata, Blessing Oburududu 'yar Najeriya ta cancanci zuwa wasan kusa da na karshe. Kuma idan ta tsallake wannan zagaye na gaba da za ta kara da 'yar Mongoliya Battsetseg Soronzonbold, za ta tabbatar wa da kasarta Najeriya lambar zinare ta farko a wannan gasa.

Wasan kwallon kwando.

Tokio 2020 | Basketball Männer | Frankreich - USA
Hoto: Thomas Coex/AFP

Ai an yi waje road da 'yan matan Najeriya na kwallon kwando a hukumance bayan da suka sha kashi a hannun Japan da ci 102 da 83. Dama dai Najeriya ce kadai kasar Afirka da ta halarci gasar a rukunin mata, kuma ta samu kanta a hali na tsaka mai wuya bayan da ta kasance a rukuni daya da Amirka da ta shahara a kwallon kwando da kuma Faransa. Alal-hakika ma dai kungiyar ta Najeriya ba ta samu maki ko da daya ba a gasar ta olympic. Dama takwarorinsu maza su ma ba su kai labari ba, domin sau uku aka lallasa su duk da nasarar da suka samu a wasannin sa da zumunci a 'yan kwallon kwando na Amirka da na Arjentina. 

Dama dai Najeriya ta samu gagarumin komabayan da ba ta taba samu ba a tarihin olympick,   inda aka dakatar da yan wasan tsere kimanin goma sha daya cikin mako guda bisa amfani da kwayoyin kara kuzari. Amma abin tambaya anan shi ne ko me yasa 'yan Najeriya suka fi kowa fuskantar wannan matsalar tsakanin kasashen Afirka, kasance ana tsananta bincike tsakanin 'yan wasanta a gasar ta Olypmci? A fannin wasan kwallon hannun mata ma, Angola ba ta ji da dai ba domin an kawar da ita, bayan da ta tashi wasa da Koriya ta Kudu da ci 31-31 ko ta'ina.

Labari mai dadi a wasannin 'yan Afirka.

Tokio 2020 | Marie-Josee Ta Lou
Hoto: Du Yu/picture-alliance/Xinhua News Agency

Kwana biyu bayan samun matsayi na hudu a tseren mita 100, 'yar gundun kasar Côte d' Ivoire Marie-Josée Ta Lou ta shiga an dama da ita a tseren mita 200, inda cikin sauki ta cancanci kai wa tseren kusa da na karshe da ya gudana a wannan Litinin. Sai dai a tseren mita 1500 kuwa, 'yar Habasha da ke gudu karkashin tutar Holland wato Sifan Hassan ta samu nasarar tsallake zuwa zagaye na gaba duk da faduwar da ya yi a lokacin wannan tseren. Dama dai tana daya daga cikin 'yan wasa da suka fi jan hankali a wannan mako na biyu na wasannin olympic sakamakon fafutukar da yake yi a tsere dabam-dabam guda uku: na 1500m / 5000m / 10000m. Hasali ma ta halarci wasan karshe na tseren 5000m a wannan Litinin.

A tseren mita 100 na maza bakin alkali ya bushe 

Sunan sabon gwani na gwanayen tseren mita 100 na duniya Lamont Marcell Jacobs dan Italiya wanda ya lashe lambar zinare a mita 100 a Gasar Olympics a Tokyo, bayan samun nasara cikin dakika 9, 80. Shi da Dan Italiyan da aka haifa a Amirka ya zama dan nahiyar Turai na farko da ya ci uwas wasannin Olympic, tun bayan dan Britaniya Linford Christie a 1992. Yayin da dan galadimansa ya kasance dan Amirka Fred Kerley, shi kuwa André De Grasse na Kanada ya samu matsayi na uku. Dan Afrika ta Kudu Akani Simbine ya zama na hudu. Yayin da a bangaren mata kuwa, 'yar Jamaica Elaine Thompson-Herah ta sami zinare a cikin dakika 10,61, lamarin da ya sa ta kafa sabon tarihin na kusan shekaru 33. Dama dai ita ce ke da bajintar tseren Olympic. A yanzu dai burin da ta sa a gaba, shi ne goge bajintar wasannin guje-guje da tsalle na duniya , wanda Florence Griffith-Joyner ke rike da ita tun 1988.

Tokio | Badminton
Hoto: Dita Alangkara/picture-alliance/AP

Jadawalin lambobi da kasashen da ke gaba.
A yanzu haka dai Chaina ce ke kan gaba da lambobi 53 ciki har da zinare 24 da azurfa 15 da tagulla 14, yayin da Amirka ta kasance a sahu na miyu da zinare 20 da azurfa 24 da tagulla 16, ita kuwa Japan mai masaukin baki tana a matsayi na uku da lambobi 31 ciki har da zinare 17. A bangaren Afirka kuwa, kasar Afirka ta kudu ta fi taka rawar gani inda ta samu lambobi 3 ciki har da zinare daya da azurfa biyu. Yayin da Tunisiya ke biya mata baya da lambobi biyu ciki har da zunare daya a fannin ninkaya.

A wasan tennis Alexander Zverev an kasar Jamus mai shekaru 24 ne ya lashe gasar rukunin maza, inda ya doke Karen Khachanov na Rasha a wasan karshe. Shi dai wannan dan asalin Hamburg ya kasance a sahun farko na wadanda suka fi shahara a fagen tennis a duniya, kuma ana ganin cewar ya durfafi kasance gwani na gwanayen wannan wasa a nan gaba.