Wace irin rawa gwamnatin Najeriya ta taka a 2012 | Siyasa | DW | 31.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wace irin rawa gwamnatin Najeriya ta taka a 2012

Yayin da ake bikin shiga sabuwar shekara, gwamnati da yan adawa suna muhawara a game da aiyukan da masu mulki a kasar suka yi a shekarar da ta kare

Jim kadan bayan shiga sabuwar shekara ta 2003, muhawara ta barke a tsakanin gwamantin kasar da tace tayi rawar gani da kuma yan adawar tarayyar Najeriya da ke zargin ta da yaudara. Wasu dai sun kira ta shekarar giwaye ga tarayyar Najeriya da ‘ya'yanta suka fuskanci barazanar tsaro mafi tasiri tun bayan yakin basasar kasar na shekaru kusan 45. An dai wayi gari da zanga zangar man fetur din da tai barazanar ganin bayan gwamnatin, kafin kaiwa ga ambaliyar ruwar da babu irin ta, tare hatsuran jiragen sama mafi yawa a cikin ta, banda karuwar fatara da talauci a tsakanin al'ummarta.

To sai dai kuma an kare shekara ta 2012 cikin banbancin ra'ayi a tsakanin mahukuntan kasar da suka ce sun yi rawar gani da kuma yan adawar da ke cewar mu gani a kasa. Wani taron manema labarai na karshen shekara dai, ministan yada labaran Najeriyar, Labaran Maku ya ambato hasken wutar lantarki da sufurin jirgin kasa da kyautatauwar harkokin noma, dama batu na lafiya a matsayin banbancin gwamantin ta Jonathan da tai alkawarin kawo sauyi. Amma kuma jam'iyyun adawar kasar ta Najeriya suka ce duk yaudara ce a bangaren shugaban da suke zargi da daukar al'adar mulki irin na yaudara. Senata Lawalli Shua'aibu dai na zaman sakataren jamiyyar Can mai jagorantar adawar cikin kasar ta NNajeriya:

Nigeria / Goodluck Jonathan / Präsident

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Damar kafa gwamanti ko kuma batu na neman haki dai, daga dukkan alamu matsayin yan adawar kasar ta Najeriya dai ya harzuka gwamantin da tace yan adawa basu da kishi, sannan kuma basu ma da aikin yi cikin kasar ta Najeriya. Labaran Maku dai na zaman ministan yada labarai, kuma kakakin gwamantin kasar. Babban alkalin gaskiyar dai daga dukkan alamu na zaman talakan kasar ta Najeriya da ke shirin shiga sabuwar shekara a cikin fatan sauyi.

Sauti da bidiyo akan labarin