Vladmir Putin zai yi takara a karo na hudu | Labarai | DW | 06.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Vladmir Putin zai yi takara a karo na hudu

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayyana cewar zai tsaya takara a karo na hudu a zaben shugaban kasa na shekara ta 2018 wanda idan ya yi nasara zai yi ci gaba da yin mulki har zuwa shekara ta 2024.

Wannan sanarwa dai da shugaban na Rasha ya bayyana ta kawo karshen jita-jitar da ake bazawa a game da takararsa, a wani sabon wa'adin mulki na shekaru shidda  bayan ya kwashe shekaru 17 a kan gadon mulki.