Vladmir Poutine ya kai ziyara farko a Iran | Labarai | DW | 16.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Vladmir Poutine ya kai ziyara farko a Iran

Shugaban ƙasar Russia Vladmir Poutine,, ya sauka a ƙasar Iran, inda zai halarci taron shugabanin ƙasashen da ke kewaye da kogin Caspienne.

Wannan itace ziyara farko da wani shugaban Russia ya taɓa kaiwa a ƙasar Iran tun shekaru fiye da 60 da su ka wuce.

Kwanaki 2 kamin fara wannan ziyara Jami´an leƙen asirin Russia, sun ce sun bankaɗo wata maƙarƙashiyar harin ta´adanci da aka kitsawa Poutine a lokacin wannan ziyara, saidai duk da haka,

Shugaban na Russia ya yanke shawara gudanar da wannan ziyara.

A nasu ɓangare hukumomin Teheran, sun ƙaryata wannan rahoto.

Poutine tare da sauran shugabanin ƙasashe 4, na kewayen kogin Caspienne, za su halarci wani taron a ƙasar ta Iran, domin masanyar ra´ayoyi, a game da mu´amiloli daban-daban da ke tsakanin su.

Vladmir Poutine da takwaran sa na Iran, Mahamud Ahmadinedjad, za su anfani da wannan dama, domin tantana batun rikicin makaman nuklea.