UNICEF: Rayuwar yara na cikin bala′i a sanadiyyar yaki | Labarai | DW | 28.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UNICEF: Rayuwar yara na cikin bala'i a sanadiyyar yaki

Yara da dama sun fada cikin bala'i a sanadiyyar barazanar da suke fuskanta daga hare-hare a kasashen da suke rayuwa da ake fama da tashe-tashen hankula a sassan duniya.

A rahoton da Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ya ce batun abu ne da ya take dokokin kasa da kasa kan yin taka tsan-tsan wajen kiyaye rayuwar masu rauni a tsakanin al'umma wato yara da mata a lokacin rikici .Daraktan UNICEF Manuel Fontaine ya yi gargadi tare da yin kira na daukar mataki game da wannan barazana tare da magance matsalar yin amfani da yara wajen kai hare-hare dama bautar da su da kuma fyade da sauran laifuka da suka keta hakkin dan Adam.

Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango na daga cikin kasashen duniya da rayuwar yara ke fuskantar wannan barazana, daruruwan yara sun rasa rayukansu a sanadiyyar rikicin kasar, a Yemen kuwa yara dubu biyar ne suka mutu a rikicin kasar na fiye da shekaru biyu inji UNICEF.