UNICEF: Ana hallaka yara kanana a Siriya | Labarai | DW | 12.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UNICEF: Ana hallaka yara kanana a Siriya

Asusun yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana takaicinsa a game da yadda ake ci gaba da kashe yara kanana a yakin Siriya wanda a wannan mako ake cika shekaru takwas da fara yakin.

A cikin wani rahoton da ya bayyana Asusun na UNICEF ya ce adadin yara da aka kashe a yakin na Siriya, ya ninka da kashi 50 a shekara ta 2017 fiye da shekara ta 2016, yara kusan miliyan uku da rabi ne ke fuskantar barazanar hare-hare na bama-bamai.