1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Zaben shugaban kasa zagaye na biyu

May 28, 2023

Al'ummar Turkiyya sun fara kada kuri'ar zaben shugaban kasa zagaye na biyu domin fitar da sabon jagora wa kasar mai fama da matsalolin koma bayan tattalin arziki da tsadar rayuwa.

https://p.dw.com/p/4RuJQ
Hoto: Evrim Aydin/AA/picture alliance

Zaben zai kasance mai matukar zafi ga 'yan takarar biyu da suka hadar da shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan da ke neman wani sabon wa'adin mulki da mai kalubalantarsa Kemal Kiliçdaroglu na jam'iyar Social Demokrat da ke neman kwace goruba a hannun kuturu.

A kalla masu zabe miliyan 60 ne ake sa ran za su fito rufunan zaben da aka bude da kimanin karfe takwas na wannan safiya kuma za a rufe rufunan da kimanin karfe biyar na wannan maraice.

Hasashen baya-bayan nan na nunar da cewa zaben na iya tsawaita wa'adin mulkin shugaba Recep Tayyip Erdogan mai shekaru 69 wanda ya shafe tsawon shekaru 20 yana jan zarensa a kan gadon mulki.

To sai dai shima dan takaran adawa Kemal Kiliçdaroglu na sa ran yin nasara a zaben bayan goyon bayan jam'iyyar Kurdawa da ya samu, duk da irin korafe-korefen da ya yi kan zagon kasan da ya ce gwamnati ta yi masa a lokacin yakin neman zabe.

Ana dai sa ran samun sakamakon zaben tun a daren yau domin buda sabon badi wa kasar ta Turkiyya dake zama daya daga cikin kasashen masu karfin fada a ji a kungiyar kawancen tsaro ta NATO.