1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Turkiyya na son a hukunta masu hannu ga harin Rafah

Abdoulaye Mamane Amadou
May 27, 2024

Kasashen duniya na tsokaci kan harin da Isra'ila kai a sansanin 'yan gudun hijira nba yankin Rafah da ya rutsa da fararen hula 45.

https://p.dw.com/p/4gLjK
Hoto: Umit Bektas/REUTERS

Kasar Turkiyya ta lashi takobin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an dauki kwakwaran matakai kan firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, bayan farmakin da dakarun Isra'ila suka kai a yankin Rafah na kudancin Gaza.

Karin bayani : Turkiyya ta bukaci Amurka ta sa baki don tsagaita wuta a Gaza

Da yake jawabi a yayin wani taron da ya jagoranta a ranar Litinin, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ba za ta taba bari mahukuntan Isra'ila da ya kira marasa tausayi su sha kan harin na yankin Rafah ba.

Karin bayani :  Shugaban Erdogan na Turkiyya na ganawa da shugaban Hamas

A nashi bangare shugaban Faransa Emanneul Macron, da ke ziyarar aiki a kasar Jamus ya yi kakkausar suka ga harin da ya rutsa da fararen hula tare da kiran bangarorin biyu da su dakatar da buta wuta nan take.