1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta kori wata 'yar Jaridar Holland

Abdullahi Tanko Bala
January 17, 2019

Hukumomin Turkiyya sun tsare 'yar jaridar Holland Ans Boersma yayin da ta je sabunta takardunta na zama a Turkiyya a birnin Istanbul kafin su tasa keyarta zuwa kasarta ta asali.

https://p.dw.com/p/3BjMk
Türkei Istanbul Demonstranten protestieren gegen Verhaftung von Reportern ohne Grenzen
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Suna

Turkiyya ta sanar da korar 'yar jaridar kasar Holland Ans Boersma daga kasarta bayan ta sami bayanai cewa tana da alaka da kungiyar 'yan ta'adda.

Jaridar da ta ke yiwa aiki Het Financieele Dagblad  ta soki matakin da cewa ya keta 'yancin 'yan jarida.

Rundunar yan sandan Holland ta ki cewa uffan akan batun.

Sai dai fadar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fitar da sanarwar cewa hukumomin Turkiyya sun sami bayanan sirri daga 'yan sandan Holland game da alakar ta da wata kungiyar ta'adda sannan sun nemi bayanai game shige da ficenta a cikin Turkiyya.