Turkiya ta tura sojojinta Iraki | Labarai | DW | 05.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta tura sojojinta Iraki

Iraki ta ce jibge sojojin Turkiya a kusa da birnin Mosul na kasar ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Fouad Massoum shugaban kasar Iraki

Fouad Massoum shugaban kasar Iraki

Shugaban kasar Iraki Fouad Massoum ya bukaci kasar Turkiya da ta janye daruruwan sojojinta da ke kusa da arewacin birnin Mosul. Massoum ya bayyana jibge sojojin na Turkiya a kasarsa da cewa ya sabawa dokokin kasa da kasa kana zai iya iza wutar rikici a yankin. A wata sanarwa da aka yada ta kafar sadarwa ta Internet, Massoum ya bukaci ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Irakin da ta yi duk mai yiwuwa wajen kare kan iyakokin kasar da kuma tabbatar da cikakken 'yancin da Irakin ke da shi. Wata majiyar tsaron kasar Turkiyan ta sanar da cewa Ankara ta tura daruruwan sojojinta zuwa Irakin ne domin bai wa sojojin kasar horo a kusa da birnin na Mosul.