Turkiya ta kaddamar da kamen ′yan Kungiyar IS | Labarai | DW | 09.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta kaddamar da kamen 'yan Kungiyar IS

Mahukuntan Turkiya sun kama mutane sama da dari da suke zargi da kasancewa 'ya'yan Kungiyar IS a lokacin wani samame da 'yan sanda suka kai a cikin birnin Ankara da kewayensa a wannan Alhamis

Mahukuntan Turkiya sun kama mutane sama da dari da suke zargi da kasancewa 'ya'yan Kungiyar IS. Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar ta Anadolu wacce ta ruwaito labarin ta ce an kama mutanen ne a lokacin wani samame da 'yan sanda suka kaddamar tun da sahin safiyar wannan Alhamis a cikin birnin Ankara da kewayensa. 

Mutane 245 ne wadanda ake zargi da kasancewa 'ya'yan Kungiyar ta IS, mahukun Turkiya suka ba da sammacin kamo su, inda daga ciki aka kama ya zuwa yanzu 111 a yayin da 'yan sanda ke ci gaba da farautar sauran. 'Yan sanda dubu da 500 ne mahukuntan Turkiyar suka baza a cikin wannan aiki samame wanda ko baya ga mutanen da suka kama 'yan sandan sun kuma kama tarin takardu da ke da alaka da Kungiyar ta IS. 

Kazalika 'yan sandan sun kuma kama wasu mutane 27 da suka hada da wasu 'yan Siriya a lokacin wani samamen na daban da suka kai a wannan Alhamis a garin Bursa na Arewa maso Yammacin kasar.