1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya na ci gaba da fafutikar zama mambar EU

Yusuf Bala Nayaya
March 26, 2018

Shugaban kasar Turkiya Tayyip Erdogan ya bayyana a wannan Litinin cewa kasarsa za ta nemi mambobin Kungiyar Tarayyar Turai su janye duk wani nau'i na tarnaki ga shirin shigar kasarsa ta zama mamba a kungiyar ta EU.

https://p.dw.com/p/2v13X
Türkei Präsident Recep Tayyip Erdogan besucht Grab von Necmettin Erbakan
Hoto: picture-alliance/AA/Turkish Presidency/Y. Bulbul

Erdogan ya bayyana haka ne gabannin tafiyarsa zuwa taron kolin kungiyar a Bulgeriya. Ya ce zai kuma tabo batun abin da ya kira gazawar kasashen na Turai wajen cika alkawuran da suka dauka a dangane da 'yan gudun hijirar Siriya. Taron kolin dai za a yi ne a gabar tekun Varna gefen Bahar Asuwad.

Turkiya dai na ci gaba da matsa lamba wajen ganin an cusata cikin kungiyar kasashen na Turai duk da irin turjiya da take fiskanta a tattaunawar da ake da ita kan batun.