1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tuhumar shugabannin NFF a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
May 28, 2019

Cikin tuhumar da ake wa shugabannin har da karkatar da sama da Dala miliyan takwas kudi daga FIFA da aka bayar a shirin wasannin duniya na 2014 a Brazil.

https://p.dw.com/p/3JLrg
Nigeria Fußball Logo Nigeria Football Federation NFF
Hoto: Franck Fife/AFP/Getty Images

Wata babbar kotu a Najeriya ta umarci wasu manyan shugabanni a hukumar da ke tsara wasannin kwallon kafa a kasar NFF su fuskanci shari'a kan badakalar cin hanci da rashawa duba da yadda ake zarginsu da karkatar da makudan miliyoyi da aka tanada don inganta harkoki na wasanni a kasar.

Shugaban hukumar wasannin kwallon kafa ta kasa a Najeriya NFF Amaju Pinnick da wasu 'yan uwansa hudu ne dai ake tuhumarsu kan laifuka 17 da suka shafi badakalar kudade. Sauran wadanda ake zargin su ne Seyi Akinwunmi mataimakin shugaba da Shehu Dikko da babban sakatare Mohammed Sanusi da Ahmed Yusuf da ke zama mamba a kwamitin zartarwa.

Mai shari'a Ifeoma Ojukwu ta ba da umarni mutanen su bayyana a gaban kuliya ranar daya ga watan Yuli don kare kai kan zargin da ake masu da ya hadar da rashin bayyana kadarori da karkatar da sama da Dala miliyan takwas da hukumar wasanni ta duniya FIFA ta bayar a shirye-shiryen wasan duniya na 2014 a Brazil.