Tsohon shugaban kasar Turkiya ya rigamu gidan gaskiya | Labarai | DW | 17.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban kasar Turkiya ya rigamu gidan gaskiya

A wannan Laraba ce (17.06.2015) tsohon shugaban kasar Turkiya Suleyman Demirel ya rigamu gidan gaskiya bayan da ya yi fama da cutar matsalar nunfashi.

Suleyman Demirel

Suleyman Demirel

Rahotanni daga birnin Istanbul na kasar Turkiya na cewa, tsohon shugaban kasar kuma wanda yake tsohon Firaminista ne a kasar ta Turkiya Suleyman Demirel dan shekaru 90 da haihuwa, ya rasu ne a wani babban asibitin birnin Ankara bayan da ya yi fama da matsalar nunfashi.

Shi dai marigayin wanda magoya bayansa ke kira Baba, an haifeshi ne a shekarar 1924 kuma ya shafe kimanin shekaru 40 a cikin harkokin siyasar kasar ta Turkiya. Ya jagoranci kasar na shekaru goma sha daya da rabi, inda ya jagoranci gwamnatoci da dama daga shekarar 1965 kafin daga bisani ya samu mukamin shugaban kasar ta Turkiya daga shekarar 1993 zuwa shekara ta 2000 kuma a karshen wa'adin mulkinsa ya sauka, sannan kuma ya ci gaba da ba da tashi taimako ta hanyar shawarwari ga 'yan siyasar kasar.