1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan Tsohon Firaiministan ya rasu

Abdul-raheem Hassan
November 26, 2020

Sadiq al-Mahdi ya kwanta dama bayan fama da jinya a asibitin hadaddiyar daular Larabawa, bayan kamuwa da cutar Corona. Za a yi jana'izarsa a ranar Juma'a a birnin Omdurman.

https://p.dw.com/p/3lqJt
Sudan Sadiq Al-Mahdi
Hoto: Getty Images/A. Shazly

Marigayi al-Mahdi shi ne zababben Firaiminista na karshe a kasar Sudan sama da shekaru 20, bayan da tsohon Shugaban kasar Omal al-Bashir ya kawar da shi a shekarar 1989. Sadik al-Mahdi ya rasu yana shekaru 84.  

Ya kasance babban mai adawa da tsohuwar gwamnatin Sudan da aka yi wa juyin mulki. A shekarar 2018 ne al-Mahdi ya koma Sudan bayan dogon lokaci yana gudun hijira a birnin Alkahira na kasar Masar, ya bar Sudan bayan takun saka tsakaninsa da gwamnatin al-Bashir ya yi zafi kan yadda yake samun karbuwa sakamakon jagorantar muryoyin al'umma domin nuna fushinsu kan matsin tattalin arziki a Sudan.

 'Yarsa Mariam mataimakiyar jam'iyyar Umma Party, na cikin wadanda aka tsare bayan gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin tsohon Shugaba al-Bashir.