Tsoffi zun zarta matasa a shan kwayoyi | Labarai | DW | 26.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsoffi zun zarta matasa a shan kwayoyi

Hukumar Kula da Magunguna ta Duniya ta baiyana fargaba kan matsalar shaye-shayen kwayoyi a tsakanin tsofaffi a Najeriya da Indiya.

Mu'amala da miyagun kwayoyi a tsakanin tsoffafi ya kai wani mizani da ake ganin wata annoba ce ta boye da ya kamata a dauki matakin magance ta. Hukumar Kula da Magunguna ta Duniya (INBC) ce ta sanar da hakan a wani sabon rahotonta da ta fitar a jiya Alhamis. Yayin gabatar da rahoton a birnin Vienna, hukumar ta ce ta gano yanda shan kwayoyi a tsakanin masu yawan shekarun ya zarta na matasa.

Hukumar ta kara da cewa, abin damuwan, shi ne, gwamnatocin ba su ma fahimci munin lamarin da illolinsa ga rayuwar masu yin ba. A yayin da binciken ke cewa, wannan matsala ta yi kamari a Amirka, a kasashen Indiya da Najeriya ma, masu shekaru tsakanin sittin da sittin da biyar na kwankwadar maganin tari na ruwa ko shan hade-haden magunguna masu kashe kaifin ciwo, ba tare da umarnin likita ba, wanda daga bisani ke hanzarta tsuffansu tare da haifar da cututtuka kamar na suga dana hanta da sauransu.