1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan ta Kudu

An rufe makarantu saboda tsananin zafi a Sudan ta Kudu

Abdoulaye Mamane Amadou
March 16, 2024

Hukumomi a kasar Sudan ta Kudu sun bayar da sanarwar rufe makarantun bokon yankuna da dama sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta.

https://p.dw.com/p/4do4F
Hoto: AFP

An samu mutane da dama da suka mutu a Sudan ta Kudu sakamakon tsananin zafi da ake fama da shi, lamarin da yakai mahukuntan daukar wannan mataki da ke zaman irinsa na farko a tarhin kasar.

Masu hasashen yanayi a kasar sun gargadi jama'a musamman ma masu rauni, da su rika boye kansu saboda zafi mai maki 45 a ma'aunin zafi da ake samu akai-akai a kasar ta Sudan ta Kudu da tun da jimawa yaki ya daidaita.

Ko baya ga tsanainin zafi, Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan ta Kudu nada mabukata agajin gaggawa akalla miliyan tara, daga cikin al'uimmar kasar miliyan 11.