Tsammanin kayan agaji a Yemen | Labarai | DW | 07.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsammanin kayan agaji a Yemen

Asusun UNICEF ya bayyana cewa sannu a hankali al'umma na kara shiga hali na kaka na kayi a kasar ta Yemen.

Kwamitin kasa da kasa da ke aikin agaji na Red Cross ICRC ya shirya tashin wasu jiragen makare da kayan agajin magunguna da ya kai tan 48 da za a yi amfani da su wajen bada tallafi a Yemen cikin kwanaki biyu da suke tafe.

Daruruwan mutane ne dai suka halaka yayin da dubbai aka tilasta musu kaurace wa mahallansu, wasu kasashe kuma ke kwashe mutanensu kain da nain cikin fadan da ya yi tsamari a 'yan kwanakinnan a kasar ta Yemen.

Tun dai a ranar Litinin ne Asusun Tallafin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa sannu a hankali al'umma na kara shiga hali na kaka na kayi a kasar ta Yemen.

Har yanzu dai ana ci gaba da cece ku ce tsakanin jami'an kwamitin na ICRC da mahukuntan kasar Saudiyya da ke jagorantar kawancen dakarun da su ke lugudan wuta kan mayakan na Houthi a Yemen kusan makwanni biyu kenan.

Mai magana da yawun kwamitin na ICRC Marie Claire Feghali ta bayyana cewa sun shirya tashin jirgin na farko da zai dauki kaya tan 16 na kayan magunguna daga Jordan zuwa Yemen a gobe Laraba.

Wasu rahotanni da ke shigowa yanzu kuma na cewa wasu da ake zargin 'yan Al-Kaida ne sun afkawa dakarun soji da ke aiki a tsakanin iyakar kasar Saudiyya da kasar ta Yemen inda suka kashe soja biyu a lardin Hadramawt tare da kwace wani sansanin soja.