Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da Amirka | Labarai | DW | 31.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da Amirka

Mataimakin shugaban Amirka Mike Pence yace matakin Moscow na korar jami'an diplomasiyyarta a Rashar ba zai sa Amirkar ta sassauta matsayinta ba.

Mataimakin shugaban Amirka Mike Pence ya ce matakin Moscow na korar jami'an diplomasiyyarta a Rashar ba zai sa Amirkar ta sassauta matsayinta ba. 

Yace suna fatan samun kyautatuwar dangantaka da Rasha amma matakin diplomasiyyar na baya bayan da Rasha ta dauka ba za su sanyayawa Amirka gwiwa ba.

Pence wanda ya kai ziyara Eastonia, bayan ganawa da shugabannin kasashe uku na Baltic, ya shaidawa taron manema labarai cewa ya mika sakon shugaba Trump ga kasashen yana tabbatar musu cewa Amirka na tare da su.

Tun da farko a ranar lahadin da ta wuce shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bukaci Amirka ta rage ma'aikatanta na diplomasiyya 755 daga cikin adadin ma'aikatan diplomasiyyarta da ke Rasha a wani matakin martani ga takunkumin da Amirka ta kakabawa Rashawa. 

Putin yace muna da zabi wanda Rasha za ta iya maida martani ga takunkumin Amirka. Mun maida martani ne a yanzu saboda yadda Amirka ke kara dagula dangantakar da ke tsakanin mu.