Tsallen badake kan sarauta a Kano | BATUTUWA | DW | 09.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Tsallen badake kan sarauta a Kano

A jihar Kano ana ci gaba da zanga-zanga domin nuna kin jinin matakin gwamnati na tsaga masarautar jihar zuwa gida biyar. Tuni dai gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan wannan doka.

Nigeria - Emir von Kano - Muhammadu Sanusi II (Getty Images/AFP/A. Abubakar)

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu

Koda yake dai a iya cewar aikin gama dai ya rigaya ya gama, domin kuwa tuni gwamnan Kanon Dr Abdullahi umar Ganduje ya rattaba hannu a kan wannan doka wacce a yanzu ta samar da karin sarakunan yanka 4 a Kanon. Kwana guda bayan matakin na gwamnatin Kanon, matasa da sauran jama'a sun gudanar da zanga-zanga domin nuna kin jinin wannan mataki suna masu cewar akwa dimbin batutuwan da yakamata ayi dokar gaggawa a kansu, amma ba wannan ba. Dr Hamisu Sadi Ali guda ne daga cikin jagororin wannan zanga-zanga, ya kuma ce sun yi zanga-zangar ne domin nuna fushinsu kan wannan batu. To amma a lokacin da yake sanya hannu a kan dokar, gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace ya yi wnanan abu ne da kyakyawar niyya da nufin kara karfin masarautar Kanon.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano (Salihi Tanko Yakasai)

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Akwai sauran rina a kaba

Sai dai kuma masu nuna kin jinin wannan mataki irinsu Kwamared Rabi'u Shamma na ganin cewa bayan tiya akwai wata cacar, domin bayan zanga-zangar za su kalubalanci batun a gaban kuliya, duba da cewar ya saba da kundin tsarin mulkin kasa. A bangaren masana kuma, Malam Murtala Uba na jami'ar Bayero da ke Kanon wanda kuma ke yin nazari kan al'adu da batun masarautun gargajiya, ya ce wannan mataki zai kawo rarrabuwar kan al'umma.

Tuni aka kara tsaurara matakan tsaro a sass daban-daban a birnin na Kano, domin gujewa barkewar rikici. Masu zanga-zangar dai sun gamu da cikas a daidai shataletalen gidan Murtala, bayan da tawagar 'yan sanda suka hana su karasawa majalisa har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai sun yi cirko-cirko suna addu'o'i a wannan wurin.

Sauti da bidiyo akan labarin